Jam’iyyar PDP ta buƙaci Shugaba Buhari da ya sauka daga mulkin ƙasar nan

0
140

Daga Abubakar zaharadden

Babbar jam’iyya mai hamayya wato PDP ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda zargin rashawa da akea hukumomin tarayya.

Shugaban Jam’iyyar na ƙasa Prince Uche Secondus ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai da jam’iyyar ta gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Prince Uche Secondus ya ambaci binciken rashawar da ake yi a hukumomin NDDC, MIC, NEDC, NSITF, EFCC da wasu inda ya ce da ƙyar Najeriya ke numfashi a karkashin mulkin Buhari.

Ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a kasar nan, duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari yana ikirarin yaƙi da shi, wanda hakan yana tabbatar da cewa tuni shugaban ƙasa ya yi watsi da alƙawarin da ya ɗaukarwa al’ummar ƙasar nan a shekarun 2015 da kuma 2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here