Kotu Ta Bada Umarni Ga Alison Madueke ta Gurfana a Gaban ta

0
216

Daga Salisu Hamisu Ali

Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja, a yau Juma’a ta bada umarni ga tsohuwar ministan albarkatun mai ta kasa, Diezani Alison-Madueke, da ta bayyana a gabanta domin amsa jerin tuhume-tuhumen da ake yi mata wadanda hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gabatar.

Alkaliyar Kotun, Ijeouma Ojukwu ce ta bada umarnin bayan bukatar da lauyan EFCC Faruk Abdallah ya nema.

Ojukwu ta bada umarnin akaiwa Mrs Alison Madueke sammancin ta gurfana bisa tuhumar da ake yi mata.

Hukumar EFCC dai ta soki tsohuwar Ministan bisa gujewa shari’a ta hanyar guduwa zuwa kasar Ingila.

Mai shari’ar wacce ta bada umarnin sammacin tace a wallafa shi a shafin hukumar EFCC da manyan jaridun kasar nan wanda hakan zai sa Mrs Alison-Madueke ta samu gayyatar da kotun tayi mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here