Fadar Shugaban Kasa tayi martani ga Jami’iyyar PDP

0
157

Daga Salisu Hamisu Ali

Fadar Shugaban Kasa tayi martani ga Jami’iyyar PDP bisa kiran da jami’iyyar tayi ga shugaban kasa Buhari yayi murabus.

A wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a Malam Garba Shehu ya fitar a yau juma’a tace ” a lokacin da kasashen duniya suka hadu wajen yaki da annobar dake damun kowa da kowa ita kuwa PDP ta kaddamar da talla domin dabbaka abin da ya sabawa tsarin dimukuradiya”.

Garba Shehu yace ” manufar Jam’iyyar PDP ta baya-bayan nan shine kiran da tayi ga shugaba Buhari yayi Murabus bayan shugaban kasar ya bada dama gudanar da bincike akan ma’aikatun gwamnati wadanda suka hada da Hukumar EFCC .”

Sanarwa ta jaddada cewa Shugaba Buhari bazai yi murabus ba , zai cigaba da yaki da cin hanci da rashawa.

Idan za’a iya tunawa dai Jam’iyyar PDP tayi kira ga shugaba Buhari yayi Murabus bisa zargin cin hanci da rashawa cikin gwamnatin ta Buhari.

Shugaban Jami’iyyar ta PDP na Kasa Prince Uche Secondus ne ya nemi shugaban kasar yayi murabus a wani taron manema labarai da yayi a Abuja .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here