A karo na biyu Yakubu Dogara ya sake komawa APC

0
184

Daga Abubakar zaharadden

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya koma Jam’iyyar APC.

Mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmed ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.

A yau Juma’a ne dai Yakubu Dogara tare da Gwamnan Yobe Mai Mala Buni suka kai ziyara ga Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

A 2018 ne dai Yakubu Dogara tare da wasu ‘yan majalisa suka sauya sheƙa daga APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here