Jihar Lagos Na Kashe Miliyan Daya a Kullum akan Duk Mutum Daya Mai Dauke da cutar Corona

0
188

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin jihar Lagos ta fitar da bayanan kudin da take kashewa a kullum kan masu kamuwa da cutar Corona a jihar inda tace tana kashe daga Dubu 100 zuwa Miliyan 1 akan kowanne mutum daya da yake dauke da cutar corona a kullum a cibiyoyin killace masu cutar.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana hakan inda yace jihar na kashe Naira dubu 100 a kullum akan wanda cutar bata yiwa illa sosai ba yayin da take kashe dubu dari biyar zuwa miliyan day akan wanda cutar tayiwa illa.

Yayin da yake jawabi wajen bayar da bayanai kan yaki da cutar a yau Alhamis Abayomi ya bayyana cewa kudin abinci wajen kwana da albashin ma’aikatan lafiya na daga cikin abubuwan da ake bi wajen kula da masu cutar.

Sannan yayi bayanin cewa kashi 60 na masu dauke da cutar COVID-19 a jihar sun fito ne daga kananan hukumomin Eti-Osa, Alimosho, Kosofe, Ikeja, da Oshodi-Isolo.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta kara yawan gadajen kula da masu cutar da gadajen kwanciya 220 yayin da za’a kaddamar da gadajen kwanciya 70 a yau a Ajao-Estate sai karin gadahe 150 da za’a kaddamar sati mai zuwa a Yaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here