Jami’ar Maryam Abacha Ta Bawa Daliba Yar Asalin Kano Kyautar Kudi Miliyan Daya

0
189

Daga Salisu Hamisu Ali

Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maradi kasar Nijar ta bayar da kyautar Naira Miliyan daya ga dalibar sashin koyan shari’a Miss Maryam Abdullahi Danba Daga Jihar Kano wacce ta zo mataki na daya .

Wanda ya kafa Jami’ar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne ya sanar da bada kyautar yayin gabatar da shedar kammala karatu ga daliban da jami’ar ta yaye a wani taron walima da da sashin koyan shari’a ya shirya a Maradi Kasar Nijar yau Alhamis.

Sannan yace Jami’ar ta bawa dalibar tallafin karatu domin yin digirin digir-gir a makarantar.

A cewar sa, Maryam Abdullahi Damban ta zama daliba mafi kwazo cikin dalibai 35 da suka kammala karatu a tsangayar koyon ilimin shari’a a shekarar 2020.

Hakanan, ya kara da cewa an yanke shawarar bawa Maryam kyautar kudin ne bisa hazakar da ra nuna haka kuma domin karfafa gwiwar sauran dalibai wajen mai da hankali akan karatu.

Farfesa Gwarzo yayi kira ga dukkan Daliban jami’ar da su dinga yin aiki tukuru da sadaukarwa wanda zai kai su ga samun nasarar abin da suka sa gaba na karatu.

Yayin da take mayar da martani a madadin sauran dalibai Maryam ta bayyana farin cikin ta da godiya ga hukumomin jami’ar bisa bata wannan kyauta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here