Yan bindiga sun sace ‘yan China huɗu a Calabar da ke kudancin Najeriya

0
165

Daga Sulaiman Auwal Mashal

Yan bindiga sun sace wasu ‘yan China hudu masu aikin gine-gine a jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.

Kwamishinar ‘yan sanda ta jihar, Irene Ugboh Itohan ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin.

Ta ce an kashe wani dan sanda da ke aiki da ‘yan Chinan a lokacin sace su ɗin a yankin Akampka a ranar Talata da daddare.

An tura jami’an tsaro wajen don neman ‘yan Chinan.

Har yanzu ba a san dalilin sace su din ba, amma satar mutane don karɓar kudin fansa abu ne da ya zama ruwan dare a fadin Najeriya, sannan abin bai bar kan kowa ba baƙi da ‘yan kasa.

A wasu lokutan masu satar mutanen kan kashe waɗanda suka sace idan har ba a biya kuɗin fansa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here