Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Asibiti a Jihar Plateau

0
161

Daga Salisu Hamisu Ali

Yan Bindiga sun kai hari babban Asibitin Karamar Hukumar Barkin Ladi dake Jihar Plateau.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa an hallaka jami’in tsaro daya sannan karin mutum 3 sun samu raunika wadanda suka hada da Ma’aikacin Asibitin da Jami’in yan sanda.

Shugaban Kungiyar Cigaban yankin Gashshi, Francis Chong yace lamarin bakon abu ne kuma abin da bazai misaltu ba ace wajen kula da lafiya wanda ke kula da kowa da kowa an kai masa hari ba tare da wani dalili ba.

Chong Kuma yayi nuni da cewa ma’aikata biyu da suka jikkata a harin suna karbar magani a asibitin Barkin Ladi.

Sai dai har Yanzu rundunar yan sanda a jihar ba ta yi bayani kan lamarin ba .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here