Wata Kungiya ta yabawa Hukumar Alhazai ta Jihar Kano Bisa tsarin mayarwa da Maniyyata Kudaden su

0
182

Daga Salisu Hamisu Ali

Kungiyar Independent Hajj Reporters wacce take dubawa tare da kawo rahotannin aikin Hajji da Umrah ta yabawa tsarin da hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano tabi wajen dawowa da maniyata aikin hajji na wannan shekarar kudaden su.

Wata sanarwar da jagoran kungiyar na kasa Ibrahim Muhammed ya fitar na cewa
“Kungiyar Independent Hajj Reporters tayi matukar farin ciki kan yadda hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta shigar da Jami’an tsaro, yan jarida, da kungiyoyi masu zaman kan su cikin tsarin mayarwa da Alhazai kudaden su bayan soke tafiya aikin hajjin bana daga hukumomin kasar Saudia”

Sanarwar ta cigaba da cewa ” Ba wai Kadai hukumomin da aka zayyana hukumar jin dadin Alhazan ta shigar cikin tsarin mayar da kudin ba har da samar da bayanai akan yawan kudin da aka mayar da kuma Alhazan da aka mayarwa”.

Idan za’a iya tunawa dai Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta fara mayar da kudaden ga maniyata ne a ranar Alhamis din da ta gabata.

Yayin fara shirin na mayarwa da Alhazan kudaden su Babban Sakatare na hukumar jin dadin Alhazai na Jihar Kano Muhammad Abba Dambatta ya gabatarwa da yan jarida cikakken bayani kan tsarin mayar da kudaden.

Dambatta yace ” Kusan Maniyyata 359 cikin 1, 794 suka nemi mi a mayar mu su da kudaden su wanda hakan yasan tsarin ya kammala a kananan hukumomi 10 cikin 44 dake Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here