Daga Salisu Hamisu Ali
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta dakatar da bukukuwan Babbar Sallah a Masarautu Biyar dake Jihar sakamakon cutar Corona
Sanarwar dakatarwa ta fito ne daga bakin Kwamishina yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba yayin tattaunawa da manema labarai.
Tun bayan dai nada sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Bai Samu yin hawan Bikin sallah ko daya ba sakanakon cutar COVID-19.