Shugaban Kasa Buhari na ganawar sirri da tsohon shugaban Kasa Jonathan

0
123

Daga Salisu Hamisu Ali

Shugaban Kasa Buhari Yanzu Haka Yana Ganawa da tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan cikin sirri.

Ganawar dai na gudana ne cikin fadar shugaban kasa dake Villa Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa Jonathan ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 11 na safe sannan ya zarce kaitsaye zuwa ofishin shugaban kasa Buhari .

Idan za’a iya tunawa dai Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Africa ta ECOWAS ta nada tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jagoranci tawagar sasanta rikicin siyasar kasar Mali.

Ana sa ran Jonathan zai yiwa Buhari bayani kan kokarin kwamitin nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here