Majalisar Dattawa ta bukaci Manyan Hafsoshin Tsaron Kasarnan suyi murabus

0
126

Daga Salisu Hamisu Ali

Majalisar ta yanke shawarar kira ga manyan hafsoshin tsaron kasar nan da suyi murabus ne bayan kudurin da dan majalisar dattijai mai wakiltar Barno ta Kudu Sanata Ali Ndume yayi wanda kuma shine shugaban kwamitin rundunar soja na majalisar.

Manyan hafsoshin tsaron dai sun hada da Gabriel Olonisakin, babban hafsan tsaro, sai babban hafsan soji Tukur Buratai , sai na sojan sama Abubakar Sadique da na sojan ruwa Ibok Ete Ekwe.

Duk da kiraye-kirayen da ake na sauke su Shugaba Buhari ya kara sabunta lokacin aikin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here