Kungiyar Yan Jaridu Tayi Allah Wadai da Harin Bomb a Katsina

0
66

Daga Salisu Hamisu Ali

Kungiyar Yan Jarida ta Najeriya(NUJ) Reshen Jihar Katsina, tayi Allah wadai da harin Bomb wanda yayi sanadiyar rasa rayukan yara biyar a Jihar inda suka bukaci gwmanatin jihar ta kara daukar matakan kare lafiyar Al’ummah.

Yara biyar ne dai suka rasa rayukan su yayin da mutane shida suka jikkata a wani harin bomb da aka kai kauyen Yammama dake karamar hukumar Malumfashi a jihar a ranar Asabar da ta gabata.

Kungiyar Yan Jaridun a wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugabanta Mr Tukur Dan-Ali tace gwamnati ta tabbata ta kama masu hannu cikin harin tare da gurfanar da su gaban shari’a.

Kungiyar ta kuma yi ta’aziya ga gwamnati da jama’ar jihar musamman mahaifin yaran da suka rasu Alhaji Hussani Mai Kwai.

Sannan kungiyar ta bukaci jami’an soji da su cigaba da kaddamar da hare-hare kan yan bindigar da suka addabi jihar tare da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin arewa maso yamma.

Fashewar Bomb din dai ta faru ne yayi da yaran suka je gona domin samun ciyawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here