Femi Gbajabimila Ya Bawa Akpabio Wa’adin Awanni 48

0
203

Daga Salisu Hamisu Ali

Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya bawa ministan cigaban yankin Niger Delta , Godswill Akpabio , wa’adin awanni 48 da ya bayyana sunaye da bayanan yan majalisar da suka karbi kwangiloli daga hukumar raya yankin Niger Delta.

Kakakin Majalisar na yin kiran ne yayin shugaban marasa rinjaye na majalisar Mr Elumelu yake gabatar da kudiri na bukatar majalisar ta gayyaci Akpabio domin bayyana sunayen yan majalisar da suka amfana da kwangilar.

A ranar Litinin din nan dai Minista Akpabio yayin zaman kwamitin bincike kan badakalar kudi a hukumar NDDC na Majalisar wakilai yace yawancin kwangilolin da hukumar ta bayar ta bayar ne ga yan majalisun.

“Ban taba karbar kwangila daga hukumar NDDC ba kuma na sani sauran mambobi ma haka” a cewar Gbajamila.

” Ina mai kira ga minista cikin awanni 24 zuwa 48 ya bayyana sunayen yan majalisar, kwangilolin da aka ba su da kwanan wata gami da kamfanonin”.

Femi yace rashin yin hakan zai sa ministan ya fuskanci fushin hukuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here