An Kama Mutane 60 Bisa Laifin Kin Sanya Safar Rufe Hanci Da Baki

0
103

Daga Salisu Hamisu Ali

Kwamitin Kar ta Kwana na Yaki da Cutar COVID-19 ya kama mutane 60 wadanda suka bijirewa dokar sanya safar rufe hanci da baki a jihar Ekiti.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wadanda suka aikata laifin an gurfanar da su a kotu ta musamman wacce kuma ta same su da laifin da ake tuhumar su.

Farfesa Bolaji Aluko Wanda shine shugaban Kwamitin ne ya bayyana hakan.

Aluku yace an kama wadanda suka karya dokar ne a gurare daban – daban na Birnin Ado Ekiti da suka hada da Ajilosun, Ijigbo, Old Garagr, Okesa, Fajuyi, da Basiri.

“Anci tarar kowannen su Naira Dubu Biyar bisa samun su da laifin kin sanya safar rufe hanci da baki a cikin jama’a kamar yadda sabuwar dokar hana yaduwar cututtaka ta tanada. Inji shi.

Sannan ya bayyana rashin jin dadin sa akan yadda mutane suke kin sanya safar rufe hanci da baki wacce kudin ta bai gaza da Naira 100 ba.

Hakanan ya bukaci mazauna jihar da su ka’idojin da aka shimfida na hana yaduwar cutar.

Yayin shima yake jawabj mai ritaya Janar Ebenezer Ogundana mai baiwa gwamnan jihar Ekiti shawara kan sha’anin tsaro yace an umarci jami’an tsaro su tabbatar da abin dokar.

Sannan ya shawarci masu motoci da su tabbata suna da safar yayin da za’a daidai ga tsaida da su ana bincikar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here