Za’a Binne Gawar Arotile A Ranar 23 Ga Watan Yuli – NAF

0
162

Daga Salisu Hamisu Ali

Rundunar sojan saman Najeriya ta ce za’a binne gawar Tolulope Arotile ranar 23 ga watan Yuli a mace ta farko Matukiyar jirgin saman sojan yakin Najeriya wacce ta mutu a ranar Talatar da ta gabata.

Air Commodore Ibikunle Daramola daraktan sadarwa da hulda da jama’a na rundunar ne ya sanar da hakan jiya juma’a a Abuja a wata sanarwa da ya fitar , inda yace za’a binne Arotile da cikakkiyar girmamawa ta soja.

Daramola yace babban hafsan sojin saman Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya karbi bakunci wasu daga cikin ministoci da yan majalisun dokokin kasarnan wadanda suka ziyarci hukumar a ranar Alhamis.

Inda yace sun zo ne domin yin gaisuwa bisa rasuwar jami’ar rundunar.

“Wadanda suka je ta’aziyyar sun hada da Ministan harkokin mata Dame Pauline Tallen da Ministan Yada labarai Alhaji Lai Mohammed.

” Wakilai daga majalisun dokoki wadanda suka hadar da mambobi 20 karkashin jagorancin shugaban kwamitin majalisar dattijai kan rundunar sojan sama Sanata Bala Ibn Na Alla da na Majalisar wakilai Sheho Koko su ma sun ziyarci rundunar”, a cewar sa.

Ya kara da cewa Ministan Mata Tallen yayin ziyarar ta’aziyar tace ta samu labarin mutuwar matukiyar jirgin cikin kaduwa.

Ministan tayi addu’ar ubangiji ya jikan jami’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here