Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa ta Kama Yan Najeriya 42 

0
101

Daga Salisu Hamisu Ali

Hukumar shige da fice ta kasa reshen jihar Katsina ta karbi yan Najeriya 42 wadanda aka dawo da su bayan sun shiga kasar Nijar ba bisa ka’ida ba a kokarin su na shiga yankin Turai.

Mai magana da yawun hukumar na kasa Mr Sunday James ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar jiya Juma’a a Abuja.

James yace an dawo da mutanen Najeriya ne ta hanyar ofishin Kongolam.

Yace wadanda abin ya shafa yan Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 wadanda suka ki tsayawa a tantance su kuma suka tsallaka kasar Nijar.

Mai magana da yawun hukumar yace babbbar kotun tarayya dake Katsina ta tura mutane 12 daga cikin su gidan gyran hali bisa laifin shiga kasar Nijar ba bisa ka’ida ba.

“Mai shari’a Hadiza Shagari yayin da take yanke hukunci ga mutanen tace ko su biya tarar dubu 50 ko kuma suyi zaman gidan gyran hali na watanni uku.

” Sannan ragowar mutane 30 din za’a gurfanar da su a gaban kotu idan aka kammala bincike akan su. Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here