COVID-19: Kafafen Yada Labarai na cikin matsanancin Hali – BON

0
148

Daga Salisu Hamisu Ali

Shugaban Kungiyar Kafafen yada labarai na Rediyo da Talabijin (BON) Hajiya Sa’a Ibrahim tace kafafen yada labarai na gudanar da ayyukan su cikin mawuyacin hali tun barkewar cutar Corona a kasarnan.

Hajiya Sa’a Ibrahim wacce ta kasance shugabar tashar talabijin ta Abubakar Rimi ta bayyana hakanne yayin taron yiwa yan jarida jawabi a shelkwatar kungiyar yan jaridu ta kasa ranar juma’a.

Inda tace gidajen rediyo da talabijin na shan matukar wuya wajen samun kudaden da za kashe kan abubuwan da suka zama wajibi sakamakon annobar Corona wacce ta jawo tabarbarwar al’amarin tattalin Arziki a Kasarnan.

Ta kara da cewa yanayin da ake ciki ne yasa kungiyar ta nemi gwamnati ta yafewa kafafen yada labaran kudaden sahalewa inda gwamnati ta amince da sahale kashi 60 kadai.

Hajiya sa’a tace Gwamnatin tarayya ta amince da bukatar mu amma kashi 6o ta yarda yayin da kafafen yada labaran zasu biya ragowar kashi 40″.

Shugaban kungiyar ta kuma yi bayanin cewa gwamnatin ta amince da bukatar ne bayan lura da yadda kafafen yada labarai suke taka rawa wajen samar da damarmakin aiki ga matasa a kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here