Yan’sanda a Jihar Bauchi na Neman Mahaifiyar Jaririyar da aka jefar da gawar ta

0
107

Daga Salisu Hamisu Ali

Yan sanda a jihar Bauchi sun ce sun fara bincike domin gano mahaifiyar wata jaririya da ta rasu kuma aka jefar da gawarta a birnin jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar DSP Ahmed Wakili ne ya fadawa kamfanin dillacin labarai na kasa NAN inda yace an samu gawar jaririyar ne a Gwalameji dake jihar ta Bauchi.

“An samu gawar jaririya da safiyar nan a Gwallameji sannan al’ummar yankin sun sanarwar da ofishin yan sanda dake Yelwa”.

” Mutanen mu sun je wajen kuma sun dau hotunan gawar wacce ta fara rubewa”

“Mun fara bincike kan lamarin kuma ana kan kokarin gano masu hannu akan lamarin” cewar Wakili.

Malam Sanusi Sani shugaban al’umma na yankin Gwallameji ya fadawa kamfanin dillacin labarai na kasa cewa mataimakin sa ne ya sanar da shi faruwar al’amarin.

“Maganar Gaskiya ina cikin bacin rai kan abinda idona ya gane min irin hakan ya taba faruwa a shekarun baya inda aka jefa yarinya cikin rijiya.

” Wannan abun damuwa ne sosai saboda yawancin mutane suna bukatar samun ya’ya amma anan muna ganin yadda Ubangiji yake bawa wasu ya’ya amma suke kashe su”

“Hakan na nuna rashin godiya ga Allah ni da al’ummata bamu ji dadin hakan ba” a cewar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here