Kungiyar Yan Jaridu Reshen Jihar Bauchi ta dakatar da dakko rahoton Kungiyar Matasan APC

0
131

Daga Salisu Hamisu Ali

Kungiyar yan jaridu ta kasa (NUJ) reshen jihar Bauchi ta dakatar da kafafen yada labarai daga dakko dukkan wani rahoto da ya shafi harkokin kungiyar matasa ta jam’iyyar APC a jihar.

Kungiyar ta sanar da dakatarwar ne ta hannun sakataren ta Malam Isah Gadau a wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis.

Sanarwar tace an dakatarwar ta biyo bayan hargitsn da ake zargin matasan APC din sun tayar yayin taron manema labarai a jihar Bauchi.

Kungiyar tace rikicin ya haifar da samun raunika ga yan kungiyar tare da lalata kayan aikin su.

Sannan kungiyar ta jinjinawa jami’an tsaro bisa daukar matakin gaggawa da suka yi wajen shawo kan lamarin .

Yayin da yake mayar da martani kan lamarin sakataren yada labari na jam’iyyar Malam Adamu Jalla yace bashi da masaniya akan taron manema labaran inda yace wadanda suka tada hayaniya a wajen ba yan jami’iyyar bane.

Yayin da yake tabbatar da faruwar Al’amarin, kakin rundunar yan sanda ta jihar Bauchi Ahmed Wakili yace lamarin abin takaici ne inda yace an dau matakin da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here