Kamfanin KEDCO Ya Musanta Batun Hukumar Samar da Ruwan sha ta Kano

0
152

Daga Salisu Hamisu Ali

Kamfanin rarrabawa hasken wutar lantarki na Kano (KEDCO) ya musanta ikirarin hukumar samar da ruwan sha ta jihar na cewa rashin wadatacciyar wutar lantarki ne ya haddasa matsalar karancin ruwan sha a jihar Kano.

A wata sanarwa da babban jami’in sadarwa na kamfanin Mr. Ibrahim Sani Shawai ya fitar kuma aka aikowa jaridar PRIME TIME NEWS ta bayyana yadda kamfanin na KEDCO Ya rarraba wuta ga madatsar ruwa ta Tamburawa a watannin Afrilu da Mayu da kuma yadda aka bayar da wutar a challawa a watan Yuni inda kamfanin yace madatsun ruwa na Tamburawa da Challawa suna samun wutar awannin 20 zuwa 23 a kowacce Rana.

Sanarwar ta kara da cewa hanyar bada wuta ta challawa na daga cikin hanyoyi masu muhimmanci dake samun wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here