Mazauna Kano Na Kukan Rashin Ruwan Fanfo

0
131

By Salisu Hamisu Ali

Al’ummmar Kananan hukumomin Dala, Nasarawa, Tarauni, Ungoggo da Kumbotso na fama da matsalar karancin ruwan fanfo.

Yayin da yake karin haske kan matsalar shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano Injiniya Garba Ahmad Kofar Wambai yayi bayanin cewa rashin tsayayyiyar wutar lantarki a madatsar ruwa ta Tamburawa ne ya hadda sa karancin samun ruwan.

Injiniya Garba na fadi hakanne ta bakin Injiniya Garba Ahamad Bichi mak kula da sashin injiniyoyi na hukumar inda yace hukumar ta samar da kudade domin tafiyar da aikace-aikace na madatsar ruwan.

Hakanan ya kara da cewa hukumar samar da ruwan sha ta jihar tana bawa kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO kudi sama da Naira Miliyan 150 duk wata , amma kamfanin baya samar da isasshiyar wuta ga madatasar ruwan illa suna samun wuta ta awannin 8 zuwa 10 a kullum.

Shugaban hukumar ya kuma ce hukumar ta tattara harajin kudi sama da Miliyan Dari biyar cikin wata daya.

Hakanan akan batun matsalar rashin ruwan Majalisar dokoki ta jihar Kano ta kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki musabbabin matsalar.

Abubakar Danladi dan majalisa mai wakiltar Gaya ne ya gabatar da kuduri a gaban majalisar inda yace rashin samun ruwan fanfo a yankin yasa al’umma cikin yanayin damuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here