Gwamnatin Jihar Kano ta Shirya Hana Kasa Kaya akan Hanyoyi

0
270

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamitin ko ta kwana da zai yi maganin masu kasa kaya akan hanya a cikin kwaryar birnin Kano.

Kwamtitin dai na karkashin shugabancin shugaba hukumar dake kula da zirga-zirgar ababan hawa na Kano(KAROTA) Baffa Babba Dan’agundi, da kuma wakilci daga rundunar tsaro ta farin kaya(DSS) da rundunar yan sanda, Civil defence da kuma hukumar kula da tsaftar muhalli ta Kano.

yayin da yake yiwa yan jarida jawabi jim kadan bayan rangadin duba wasu kasuwanni na cikin birni shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Dan’agundi yayi zargin cewa masu kasa kaya akan hanya sun ki shiga cikin kasuwanni amma suna gudanar da harkokin su ba bisa ka’ida ba.

Inda ya kara da cewa sababbin kasuwannin Sabuwar Tasha, Ungoggi, Kofar Ruwa da Rukunin Masana’antu na Nasarawa an gina su ne tsawon shekaru goma da suka wuce amma masu shagunan sun ki zuwa domin yin kasuwanci a chan.

Shugaban na KAROTA yace kasuwannin na da shaguna sama da dubu biyar tare da tsaro da abubuwan bakatu.

Sannan yayi karin bayanin cewa Gwamnatin Kano ta bayar da wa’adi ga masu harkokin kasuwanci ba bisa ka’ida ba a kasuwar Sabon gari, Kasuwar Singer, da Wapa yan babura da su koma wadanchan kasuwanni da aka tanada.

Daga Karshe yayi alkawarin cewa matukar yan kasuwar suka koma wadanna kasuwani da ak tanada za su sami kariya da dukkan abinda suke bukata domin yin kasuwanci cikin tsarin bin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here