Kwananan Zamu Kawo Karshen Cutar Corona a Kano, inji Ganduje

0
124

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin Jihar Kano ta bugi kirjin cewa nan da yan kwanaki za ta kawo karshen cutar Corona a Kano.

Gwamman Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne yayi ikirarin hakan biyo bayan samun raguwar masu kamuwa da cutar a jihar.

Ganduje na fadin haka ne yayin bude sabuwar cibiyar killace masu cutar a garin Yargaya a yau Talata, inda yace yanayin da ake ciki yanzu a jihar ya nuna cewa an kusa ganin bayan cutar a Kano.

Shima wanda ya gyara cibiyar ta Yargaya Mudassir Idris Mai Kamfanin Mudassir & Brothers cewa ya yi yayi aikin gyaran cibiyar ne yayin da yaji gwamna Ganduje na yin kira masu hannu da shuni wajen taimakawa a yakar cutar corona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here