Matasa Sama da Miliyan 4 ne Suka Nemi Shiga Shirin Npower Cikin Kwana 16

0
109

Daga Salisu Hamisu Ali

Ma’aikatar jin kai da wal-walar jama’a ta kasa tace shafin ta na daukar ma’aikatan Npower yan rukunin C ya karbi bukatar mutane Miliyan 4.48 da suke son shiga cikin shirin.

Ministar Ma’aikatar jin kai da wal-walar jama’a Hajiya Sadiya Faruq ce ta sanar da hakan a shafin ta na Twitter a daren ranar Lahadi.

Ministan tace “Ni da tawagata muna cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da samun nasarar shirin Npower . Kusan kwana 16 kenan da bude shafin inda zuwa yau mun karbi mutane Miliyan 4.48 da suke son shiga cikin shirin.

Ma’aikatar dai ta fara aikin dibar sabbin wanda zasu amfana da shirin yan rukuni C a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Sai dai Ma’aikatar tace mutane dubu dari hudu kadai za’a dauka a cikin shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here