Tsohon Minista, Shamsu Ya Fara aiki da Cibiyar aikin Jarida da koyan mulki ta Dantiye

0
133

Daga Salisu Hamisu Ali

Shamsudden Usman, tsohon minista a lokacin gwamnatin marigayi Shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ya fara aiki tare da cibiyar samar da kyakkwawan shugabanci da aikin jarida ta Dantiye Center for Good Leadrship and Journalism(DCLJ).

Dakta Usman, a wani jawabi na fara aikin nasa da ya fitar a jiya Alhamis ta cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban cibiyar Emeritus Farfesa Munzali Jibril.

Farfesa Jibril Yace matakin da cibiyar ta dauka na nada Usman a matsayin mai bada shawara kan sha’anin tattalin arziki ga cibiyar an dauke shi ne bisa “irin gudunmawar da ya bayar wajen habakar tattalin arzikin Najeriya da ma Afrika ta yamma, sannan kuma saboda kaunar sa ga hidimtawa kasa”.

Sannan yace yana fatan Dr. Shamaudden Usman wanda ya kasance Ministan kudin kasarnan tsakanin shekarar 2007 zuwa da 2009 zai yi amfani da kwarewar sa domin cigaba da rainon matasa masu tasowa da kuma dakile irin matsalolin da suke fuskantar kasarnan.

DCLJ dai Kamfani ne mai zaman kansa wanda ya hada kwararru wadanda suke kokarin samar da shugabanci na gari da kuma aikin jarida na kwarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here