An bi Ka’idojin Kariya daga cutar COVID-19 A filin Sauka da tashin Jirage na Malam Aminu Kano

0
127

Daga Salisu Hamisu Ali 

Daruruwan Fasinjoji ne suka bi ka’idojin kariya daga cutar Corona a jiya a Asabar a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano yayin da aka dawo jigilar jiragen sama a cikin gida inda jiragen Azman Air da Max Airlines suka dau fasinjoji.

An ga dai fasinjoji na bin layi tare da ba da tazara da kuma kula da sauran ka’idojin da aka shimfida.

Idan za’a iya tunawa dai Gwamnatin tarayya ta bada umarnin sake dawowa da tafiye-tafiye ta jirgin sama tsakanin jihohi a ranar 8 ga watan Yulin da muke ciki bayan an dakatar da hakan a ranar 30 ga watan Maris.

Jaridar PRIME TIME NEWS ta lura da cewa an samu karin kudin jirgi sannan kuma kadanne daga jiragen suka dawo aiki a ranar Asabar.

Sannan a shaidawa Jaridar ta PRIME TIME NEWS cewa karin kudin jirgin ya samu ne sakamakon karin harajin da hukumar dake kula da filayen jiragen sama ta kasa ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here