Malami Ya Nemi Abokan Arziki da su zauna a gida ba sai sun halarci bikin Dan sa ba

0
189

Daga Salisu Hamisu

Daurin Auren dan gidan Antoni Janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami ya gudana bisa bin ka’idoji da tsare-tsaren da kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da annobar COVID-19 ya shimfida.

Ministan ya godewa abokan arziki , da masu addu’ar fatan alkhairi bisa addu’o’in su ga daurin auren dan sa wanda aka yi a Jihar Kano.

Malami ya bayyana farin cikin sa bisa fahimtar cewa sakamakon annobar corona taron bikin anyi shi a takaice.

Tun da farko sai dai ministan ya nemi abokai da yan’uwa suyi addu’a ga fatan alkhairi ga bikin basai sun halarta ba sakamakon fama da annobar corona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here