Gwamnatin Kano ta amince da samar da filaye domin yin abincin dabbobi

0
126

Daga Salisu Hamisu

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da bada ma girman hectares 1000 domin samar da abincin dabbobi karkashin shirin cigaban ayyukan gona na Kano.

An amince da karin filayen ne a kananan hukumomi 16 dake jihar .

Babban mai kula da shirin cigaban ayyukan gona na kano Malam Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana hakan jim kadan bayan tattaunawa da tawagar jami’an gwamnati karkashin jagorancin babban sakatare na ma’aikatar aikin gona Alhaji Adamu Abdu Faragai a Kano.

“Amincewa gwamnati na bada wannnan fili zai bada damar fara zuba hannun jari a fannin samar da abincin dabbobi tare da hadin gwaiwar kamfanoni masu zaman kan su” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here