Gwamanatin Kano ta ware kudi Biliyan 5 Domin yakar cutar Malaria

0
264

Daga Salisu Hamisu Ali

Gwamnatin jihar Kano tace ta ware kudi Naira Biliyan 5 domin yaki da cutar Maleria a jihar.

Sannan tace an ware miliyan 100 domin bunkasa lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yayin sanar da fara kamfen na kariya daga cutar Malaria mai suna (SMC) da kuma makon mata masu juna biyu da kananan yara (MNCH) domin rage yawan samun mace-mace tsakanin mata da kananan yara a jihar ta Kano.

Tsanyawa yace yara miliyan uku yan kasa da shekara 5 ake saran shirin zai shafa wanda za’ayi shi a kananan hukumomi 44 dake jihar.

Hakanan Kwamishinan ya koka kan yadda ba’a amfani da gidan sauro mai dauke da magani inda yace “gwamnati ta raba gidan sauro miliyan 8 a shekarar da ta gabata sai dai damuwar shine duk da mutane sun mallake shi amma basa amfani da shi , ya kamata mutane su dinga amfani dashi domin kare kan su.”

“Akwai bukatar hadin kai domin tabbatar da an wayar da kan al’umma yadda zasu yi amfani da gidan sauron” inji Dr. Tsanyawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here