Ban Siya Da na Kowanne irin gida ba a Abuja – Malami

0
183

An daura auren babban dan ministan shari’a kuma Antoni Janar na kasa Abubakar Malami a Kano da safiyar wannnan rana ta 11 ga watan Yuli.

Sai dai a sanarwar da mai taimakawa Ministan kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a Dr.Umar Gwandu ya fitar
Ministan ya musanta labaran da jaridar Sahara Reporters ta wallafa na cewa ya siyawa dan nasa gida na kudi Naira Miliyan 300 a Abuja.

Malami yace “Allah Ya sani ban siya da na gida a Abuja ba kuma ban nema masa ko da hayar gida a Abuja ba Saboda bashi da bukatar rayuwa a Abuja”.

Sannan Ministan ya karya batun hayar jirgi na musamman domin zuwa daurin auren dan na sa , sannan yace anbi dukkan ka’idojin da aka shimfida na yaki da cutar Corona yayin bikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here