Aikin Samar da tashar Wutar Lantarki a garin Bichi Zai bunkasa tattalin Arziki…Ganduje

0
165

Daga Salisu Hamisu

Gwamman Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi nuni da cewa sabuwar tashar hasken wutar lantarki da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ta Najeriya ya samar a garin Bichi dake karamar hukumar Bichi a Kano zai taimaka wajen dawo da bunkasar tatttalin arziki bayan annobar COVID-19.

Sannan yace “Aikin zai samar da tsayayyar wutar lantarki ga kananan hukumomi bakwai dake yankin wanda hakan zai taimaka bunkasa harkokin kasuwanci”.

Gwamnan yana fadin hakanne yayin da yake karamar manajan Darakta na kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Najeriya Injiniya Sule AbdulAziz , wanda ya kai masa ziyara a ofishin sa dake gidan gwamnatin jihar Kano jiya Juma’a.

Idan za’a iya tunawa dai Gwamnatin tarayayya ta hannun ma’aikatar wutar lantarki a kwanannan ta amince da samar da tashar a garin Bichi.

Gwamna Ganduje ya godewa shugaban Kasa Buhari tare da ministan wutar lantarki bisa kokarin su wajen tallafawa jihar Kano domin farfado da tattalin arzikin ta bayan fama da annobar Corona.

Yayin da yake jawabi Manajan darakta na kamfanin Injiniya AbdulAziz cewa yayi yazo Kano ne domin yadda aikin ke tafiya inda ya bayyana cewa abin da ya gani ya gamsar da shi cewa gwamnatin Kano ta himmatu wajen ganin kammaluwar aikin cikin nasara.

” Da zarar an kammala aikin gine-gine bazai dauke ba wata uku ba zamu kammala samar da tashar.” Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here