Shugaban Kasa Buhari Ya Dakatar da Magu

0
231

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Ibrahim Magu a matsayin mai rikon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati wato (EFCC), domin bada dama ga kwamitin bincike na fadar shugaban kasa a binciken da ake yi masa.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwar da Dr. Umar Gwandu mai taimakawa ministan Shari’a kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a ya rabawa manema labarai a yay juma’a.

Sanarwar ta kara da cewa shugaba Buhari ya amince Daraktan ayyuka na hukumar ta EFCC Mohammed Umar ya cigaba da rike hukumar har sai an kammala binciken da ake yi da kuma daukar mataki na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here