El-Rufai Ya Sanya Dokar Tabaci Kan Tsaftar Muhalli a Jihar Kaduna

0
182

Daga Salisu Hamisu

Gwamanatin Jihar Kaduna ta sanya dokar tabaci akan samar da tsaftaccen Ruwan sha tare da tsabtar muhalli.

Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kaduna Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakan a jiya Alhamis.

Inda yace matakin zai baiwa jihar damar samun nasara wajen samar da tsabtaccen muhalli, da ruwan sha .

Adekeye yayi bayanin cewa jihar ta kuduri aniyar dakatar da yin bayan gida a bude a fadin kananan hukumomin jihar 23.

Mai magana da yawun gwamnan ya kara da cewa wasu matakai da gwamnatin jihar ta dauka domin cimma wannnan buri sun hadu da samar da fanfunan burtsatsai guda 110 a fadin jihar a shekarar 2019

Sannan yace a wannan shekarar ta 2020 hukumar RUWASSA a jihar ta Kaduna ta samar da Rijiyar Burtsatsai 216.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here