Inshorar Lafiya Ga Ma’aikatan Yada Labarai, Babbar Nasara Ga Aikin Jarida

0
221
Daga Muhammad Gambo Tudun Wada
Tsahon shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa, Nigeria Union Of Journalist (NUJ) a takaice ya bayyana samar da shirin taimakekeniyar kula da lafiyar manema labarai a matsayin babbar nasara ga aikin.
Muhammad Garba, ya bayyana haka ne a wurin taron shekara shekara na tunawa da tsohon shugaban gidan Radiyon kano marigayi Umar Saidu Tudun Wada wanda ya gudana a zauren taro na coronation hall dake fadar gwamnatin jihar Kano arewa maso yammacin Najeriya.
Muhammad Garba wanda shi ne kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Kano yace matukar yan jaridu zasu dauki akidar tara wani kaso cikin albashin su ko wanne wata, hakan zai taimaka musu da zarar wani abu da jibanci rashin lafiya ko rasa rai ya auku.
” Irin wadannan kudade idan aka tara da sune za a biya asibitocin da suka duba mambobin kungiyar, a wasu lokutan ma har da taimakawa iyalan wadanda abin ya shafa.
” Ko lokacin da nake shugabancin kungiyar NUJ ta kasa na bijiro da irin wannan tsari na inshorar Lafiya ga yan kungiya, sai dai kawo yanzu shirin ya dakata”.
A cewar kwamishinan ta haka ne kadai yanayin lafiya da walwalar ma’aikatan jarida zai bunkasa domin su samu damar gudanar da ayyukan su na ilimantarwa, fadakarwa da nishadantar da al ummah kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar.
A daya hannun kuma, Muhammad Garba ya bukaci kafafan yada labarai musamman masu zaman kansu, da su dinga biyan albashin ma’aikatan su ko wanne wata domin hakan ya zamo wata sakayya bisa irin jajircewar da suke wajen bankado gaskiya domin amfanin al ummah.
Kuma hakan na iya taimakawa wajen dakile al’adar nan ta rashin walwalar da ma’aikatan yada labarai ke fama da ita ta rashin kyakyawan yanayin aiki musamman ta bangaren kudade.
Daga bisani kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Kano Muhammad Garba ya bukaci matasan yan jaridu da su yi koyi ga halayen tsohon shugaban gidan Radiyon kano marigayi Umar Saidu Tudun Wada ta hanyar yin da gaskiya da rikon amana.
Idan za a iya tunawa dai, marigayi Umar Saidu Tudun ya hadu da ajalin sa ne shekarar data gabata, a wani hadarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar sa ta dawowa daga birnin Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here