Yankunan arewa maso yamma da maso gabas na daf da fadawa cikin matsanancin karancin lantarki

0
205

Daga Bello Muhammad , Gusau

Bisa dukkan Alamu mutanen yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas za su dandana karancin lantarki na Inna na ha, saboda lalacewar daya daga cikin manyan wayoyin Lantarki guda biyu da suka dauko wutar daga tashar Samar da lantarki ta shiroro a jihar Niger zuwa kaduna.
.
Wani maaikacin Hukumar lantarki ta kasa shiyyar kaduna dake Gusau, da ya ce a sakaya sunarsa, ya ce lalacewa ko katsewar daya daga cikin wayoyin biyu ya sa an sami raguwar karfin Lantarkin da ake turowa daga shiroro zuwa kaduna.

Tashar Adana Lantarkin ta kaduna ce ke baiwa jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Sokoto, kebbi da Zamfara da kuma daukacin jihohin arewa maso gabas da Lantarkin.

Kamar yadda wannan maaikaci ya fadi, ya ce wannan ne ya sa ba a samun isasshen Lantarkin a wadannan wuraren yadda ya kamata.

Majiyar ta kuma bayyana ma na dukkan kokarin da akai na gyarar wayar abin ya faskara saboda Yanayin rashin tsaron da ake fuskanta a jihohin Niger da kaduna.

Rahotanni dai sun ce wasu yan sanda da suka raka maaikatan Lantarkin wurin da abin ya faru, don yin gyara ya ci tura, saboda wasu yan bindigar da ke labe a dazuzzukan sun farmake su, Alamarin da ya cusa tsoro da fargaba a Tsakanin maaikatan.

Akasarin wadanda suka zanta da wakilinmu game da karuwar Alamarin sun nuna takaicinsu akan abin da ya farun, Sannan suka roki mahukunta su gaggauta dauki matakin gyara don daidaiton alamurra.

Wakilinmu da ke Gusau ya ba da labarin cewar mutanen garin na cikin tasku da kuncin rashin Lantarkin a cikin yan kwanakin nan inda ake baiwa jihar zamfara gaba daya megawatts na lantarki biyar zuwa bakwai, Wanda Sam ba ya isa.

Wannan alamari dai na neman gurgunta harkokin Rayuwa da zamantakewar alummar jihar.

Dukkan yinkurin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin jamian Hukumar Lantarkin ta kasa akan batun ya ci tura saboda sun ki yarda su ce uffan akan batun.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here