Kwamishinan lafiya na kano ya isar da taaziyya ga iyalan Ajimobi da Ganduje

0
194

Daga Sulaiman Auwal mashal

Kwamishinan lafiya Na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya taya mai girma gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje alhinin mutuwar sirikin sa kuma tsohon gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi .

Kazalika Dakta Tsanyawa ya taya iyalan mamacin da daukacin al’ummar jihar Oyo bisa rashin marigayi Sanata Abiola Ajimobi.

Yace sunyi matukar kaduwa bisa samun labarin mutuwar marigayi tsohon gwamnan jihar ta Oyo.

Harma ya bayyana shi a mtsayin mutum mai cike da kwarewa Wanda ya sadaukar da kansa domin hidimtawa kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here