Zaa gudanar da gwajin shan kwaya ga maaikata, yan siyasa da dalibai a Kano inji Ganduje

0
138

Daga Sulaiman Auwal mashal

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Yace akwai shirye shirye fara gudanar da gwajin miyagun kwayoyi ga masu rike da mukaman siyasa, ma’ikatan gwamnati da sauran daliban dake Neman izinin shiga manyan makarantun gaba da sakandire a jihar Kano.

Hakan Na kunshe ne a cikin wani jawabi da kwamishinan yada labarai Na jihar Kano malam Muhammad Garba ya fitar a wani mataki Na bikin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta duniya harma Yace da zarar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta jihar Kano ta fara aiki za’a fara gwajin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here