Karancin Masara, Ka Iya Shafar Tattalin Arzikin Najeriya – Cewar Shugaban Kungiyar Manoman Kaji Ta Kasa

0
369
Hatimin Kungiyar Manoman Kaji Na Najeriya

Daga Abubakar Zaharaddeen Kano

Shugaban kungiyar masu noman kaji ta kasa reshen jihar Kano, Umar Usman Kibiya yayi kira ga gwamnatin tarayya da da gaggauta magance matsalar karancin masara a kananan rumbuna da kasuwanni da gidajen gona wanda hakan na shafar sarrafa abincin kaji.

Kibiya wanda ya gana da manema labarai a Kano, a ranar Alkhamis, ya bayyana cewa karancin masarar sarrafa abincin kajin da sauran amfani zai iya haddasa rasa ayyuka da dama a kasar nan, “sabida haka ne yasa nake kira ga gwamnatin tarayya da ta bayar da umurnin fito da tarun masarar da aka jibge a manyan rumbunan kasar nan domin kawo karshen wannan matsala.”

“Babu shakka wannan shine lokacin da ya kamata gwamnatin tarayya ta yi amfani da masarar da ta ajiye a rumbunanta domin hakan zai taimakawa tattalin arzuki ya habaka tare da samar da ayyukan yi ga al’uma a kasar nan – duba da yadda gwamnati ta mayar da hankali akan harkar noma ta yadda za su samar da wadataccen abinci a lokacin noma da ake ciki tare kuma da tallafawa manoma da kayayyakin aikin gona na zamani da kuma taki.”

Shugaban kungiyar kazalika ya kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta iya hada hannu da ma’aikatar bunkasa aikin gona da masu ruwa da tsaki a harkar domin tabbatar da cewa an samar da isasshen abinci a kasuwannin kasar nan da gidaje da kuma wuraren kiwon kaji domin kaucewa durkushewar kasuwancin.

“Wajibi ne gwamnati tayi kira ga manyan yan kasuwa da suke boye kayan abincinsu musamman masara da su fito da ita domin kubutar da tattalin arzikin kasar nan daga lalacewa wanda hakan zai tursasawa da yawa daga cikin masu aikin gona barin sana’arsu – wanda hakan barazana ce gagaruma, a domin haka wajibi ne gwamnatin tarayya ta waiwayi manoman kaji da masu noman masara domin sarrafa abincin kaji a kasar nan.´inji shugaban PAN, Kibiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here