Ayi zaman siyasa bada gaba ba, inji Murtala Garo

0
181

Daga Suleiman Auwal Marshal

An bukaci al’ummar karamar hukumar Ungogo kan su zauna da junan su lafiya batare da yin siyasar a mutu ko ayi rai ba domin cigaban yankin.

Shugabar kwamitin sasanci Na karamar hukumar Alhaji Murtala Sule Garo shine ya bayyana haka a lokacin da yake cigaba da aikin sa Na kawo daidaito a tsakanin magoya bayan jam’iyar APC a yankin.

Yace babu shakka aikin nasa ya samu nasara ne sakamakon goyon bayan da al’ummar suke bawa kwamitin nasa.

Kazalika ya bukace su dasu kasance masu San cigaban demokradiyya a yankin dama jihar Kano baki daya.

A karshe Alhaji Murtala Sule Garo ya yabawa gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarin sa Na warware matsalar data addabi magoya bayan jam’iyar a dukkanin kananan hukumomin jihar Kano 44.

Shima anasa jawabin Dan majalissa mai wakiltar karamar hukumar Makoda kuma mataimakin shugaban majalissar dokoki ta jihar Kano Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya bayyana matukar godiyar sa bisa irin hadin kan da al’ummar ungogo suka banyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here