Akalla sama da matasa 400 ne suka amfana da tallafin a yankin karamar hukumar Kabo

0
193

Daga Suleiman Auwal Marshal

Kwamishinan kananan hukumomin Alhaji Murtala Sule Garo ne ya Samar da kungiyar domin ganin an tallafawa dubban matasa dake jihar nan wajen ganin sun zama Masu dogaro da kawunan su domin cigaban Kansu dama jiha baki daya.

Jami’in yada labaran ma’aikatar kananan hukumomin jihar nan Mallam Zahradden Usman Kofar Nassarawa ya rawaito cewa kwamishinan ya ce dukkanin wadanda suka amfana da tallafin an zabo su daga cikin karamar hukumar Kabo kuma da dama daga cikin wadanda suka amfana Manoma ne.

Anasa bangaren shugaban karaman hukumar Kabo Alh Kabir Kabo, da kuma Dan Majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kabo da Gwarzo a majalisar dokokin Jihar Kano Alh Musa Umar sun yabawa kwamishinan kananan hukumomin bisa Wannan abun alheri da yayi inda suka kuma bukaci wadanda suka amfana da tallafin zasuyi abinda ya dace da tallafin.

Anasa bangaren shugaban jam’iyar APC na karamar hukumar Kabo Alh Yahaya Hussaini ya ce kowane daga cikin wadanda suka amfana da tallafin ya samu kudi naira Dubu Ashirin domin dai Fara sanaar dogaro da kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here