Iska da ruwan sama a Kano sun kashe mutane da rusa gidaje

0
207
Daga Suleiman A.Ramat

Babban Sakataren hukumar bada agajin gaggawa na jahar Kano (SEMA) Dakta Saleh Aliyu Jili ya bayyana cewa sakamakon mamakon ruwan sama da iska da akayi a jahar an sami asarar rayuka da rugujewar xinbin gidaje a wasu sassa na qananan hukumomin jahar.

Dokta Saleh Jili wanda ya bayyana hakan da yake zantawa da wakilimmu yace tuni sun sami qididdigar  wasu daga asarar rayuka da Dukiya da aka samu a ruwan farko da akayi na wasu qananan hukumomin harma sun ziyarci wasu daga cikinsu sunyi musu jaje a madadin Gwamnatin Kano tare da basu kayayyakin tallafi dazai xan rage musu raxaxin halinda suka shiga sakamakon ambaliyar.
Yace dama ita hukumar ta “SEMA” an kafatane dan tallafawa waxanda suka haxu da Ibtila’i dan basu kulawa da tausayawa da nema masa sauqi ta basu agaji.Wanda yayi asara ba lallai bane a iya biya masa abinda ya rasa amma za’a rage masa damuwa.
Dokta Jili yace cikin asarar rayuka da aka samu akwai magidanci daya rasa iyalansa guda Biyar sakamakon ruftawar gini a unguwar Ja’en sannan akwai wani magidanci  wanda ya rasa ransa a lokacin ambaliyar sakamakon kama turken lantarki da yayi.
Ya koka da cewa yawanci irin waxannan gine-gine da suke fuskantar rugujewa ko iska ta xauke rufinsu na faruwane saboda rashin gini da rufi mai inganci da ake ba’a amfani da kayan gini masu nagarta shi yasa idan iska mau qarfi ta taso sai ta yaye rufin sannan ta rushe ginin da akayi mara inganci ko kuma yin gini ba tareda fitarda magudanan ruwa ba sai ruwa ya rusashi.
Yaja hankalin mutane su riqa daurewa suna gini mai inganci kar suyi gaggawa dazai jawo asara saboda qaguwa su mallaki muhalli da hakan kan iya jawo hasarar rai da dukiya.
Yace an sami rusau da yayewar kwanuka a qananan hukumomin Kibiya da Gwarzo sa Rimin gada da Gwale.A kibiya an sami gidaje sama da 300 duk sun rushe saboda yayewar kwanuka an kai musu kayan agaji.Rimin Gado ma samada gidaje 500 sun rushe.Yanzu sun sami rahoto daga Gabawasa ta nuna gidaje da iska ta xaukewa rufi sun kai 1,333.00.Gida 536 sun rushe.Haka aketa samu akwai wurare da yawa da suka sami bayani na varna mai yawan gaske musamman a cikin kwaryar Birnin Kano.Haka a Bichi da Ungogo sun tura jami’ansu suje su duba irin asararda akayi dan turawa Gwamnati rahoto a duba yanda za’a tallafa musu.
Dokta Sale Aliyu jili yace sun kafa babban kwamiti na masu ruwa da tsaki akan harkar annoba da iftila’i zasu riqa fita wayar dakan mutane yanda zasu riqa yashe magudanan ruwa da kariya daga faruwar ambaliya da yanda za’abi dokoki dan kariya.
Jili yayi kira ga shugabanin qananan hukumomi da ma’aikatar qananan akan su farfaxo da ayyukan gayya  da ake da  dan yana taimakawa wajen gudanar ruwa ta sayawa qungiyoyin aikin gayyar kayan aiki  hakan zai rage matsala da ake shiga.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa yace bai kamata jama’a suyi sake na cewa sai Gwamnati tayi musu ba kamata yayi al’umma su tashi su riqa taimakawa kansu saboda ba Gwamnatice zata yiwa kowa buqatunsa ba ayyuka sun mata yawa.
Dokta Alhaji Saleh Jili yace daga cikin kayayyakinda suka miqa na agajin gaggawa a qananan hukumomin Kibiya da Rimin Gado sun haxa da Buhunan shinkafa dana suminti da bandurar kwanon rufi da katan-katan na taliya da makaroni da gishiri da katifu sa tabarmi da bandura na shadda sa atamfofi da kwalayen qusar rufi dana buga rafta da maganin sauro dan rage musu raxaxi.
Babban Sakataren Hukumar agajin Gaggawar na Jahar Kano.Dokta Saleh Jili yayi kira ga masu hannu da shuni da qungiyoyin agaji su riqa tallafawa qoqarin hukumar wajen sun tallafawa waxanda ambiyar ta shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here