Gbajabiamila ya godewa likitoci da janye yajin aikin da sukayi

0
109

Daga Sulaiman Auwal Mashal

Kakakin majalissar wakilai ta tarayya Femi Gbajabiamila ya yabawa matakin da likitoci suka dauka Na janye yajin aikin da sukeyi tare da komawa bakin aiki biyo bayan kammala ganawa da wata kungiya.

Mista Gbajabiamila Yace wannan mataki Na kungiyar likitocin ya nuna yadda kasarnan ke cikin zuciyar su harma Yace zauren majalissar wakilai da shugabancin sa yana matukar yabawa da wannan mataki.

Hakan Na kunshe ne a cikin wani jawabi da mai bawa kakakin majalissar wakilai ta tarayya akan kafofin sadarwa da Hulda da jama’a Mista Lanre Lasisi ya fitar inda Yace kokarin da zauren majalissar wakilai ta tarayya yayi yayi matukar taka rawa wajen warware matsalar.

Idan za’a Iya tunawa tun a ranar 9 ga watan Juli mista Gbajabiamila ya gana da kungiay likitocin kasarnan Wanda daga bisani zauren majalissar wakilai ta tarayya ya sahale naira biliyan 4 a matsayin kudin da za a basu Na alawus alawus din su tare da tabbatar musu da cewa yana cikin kunshin kasafin kudin shekarar 2020 da akayiwa kwaskwarima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here