Obaseki ya sauya sheka zuwa PDP

0
182

Daga Sulaiman Auwal Mashal

Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamna Obaseki na jihar Edo ya sauya sheka izuwa babbar jam’iya ta PDP.

Anasa rai dai Obaseki shine wanda zaiyi takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam’iyar ta PDO.

Mista Obaseki ya isa sakatariyar jam’iyar PDP a jihar da misalign karfe 2 da mintuna 20 na rana tare da rakiyar gungun magoya bayan sa.

Tunda fari dai gwamna Obaseki ya fara tsayawa takarar gwamnan jihar ne a karkashin inuwar jam’iyar APC wadda daga bisani jam’iyar ta dakatar dashi daga tsayawa takarar fidda gwani a jam’iyar bisa zargin rashin daidaito a takardun sa.

Haka kuma kwamitin gudanarwar jam’iyar ta PDP na kasa  yace ya dage zaben fidda gwani na jam’iyar wanda suke saran yi a ranar 19 ga watan Yuni dakuma 20 ga watan na Yuni zuwa ranar 23 ga watan na Yuni.

Kazalika sakataren jam’iyar PDP na kasa Kola Ologbodiyan wanda shine ya tabbatar da wannan labari ga manema labarai hrma yace wanan na daga cikin ayyukan da jam’iyar ke gabatarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here