Ba a musgunawa mabiya addinin kirista a Najeriya, inji Buhari

0
162

Daga Sulaiman Auwal Mashal

Fadar shugaban kasa tayi watsi da rahoron da wata kungiya daga kasa Burtaniya wato AAPG wadda tace tagabatar da rahoton cewa mabiya addinin kirista na fuskantar kalubale daga kungiyoyin mahara da suka hadar da makiyaya wanda ya shafi dubbana mabiya addinin na Kirista.

Rahoton yace akwai tabbacin cewa gwamnatin kasarnan ta gaza daukar kwakwaran mataki kan hana faruwar kai harin.

Sai dai da yake maida martani kan wannan rahoto, babban mai bawa shugaban kasa shawara kan kafofin sadarwa da hulda da jama’a Malam Garba Shehu yace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na aiki kafada da kafada da dukkanin bangarorin addinan kasarnan dana hukumomin tsaro wajen wanzar da zaman lafiya.

Kazalika ya ce gwamnatin kasarnan na maraba da wadannan kungiyoyi domin zuwa kasarnan don ganewa kansu irin kokarin da gwamnatin kasarnan keyi wajen tabbatar da yanci ga al’ummar kasarnan.

Haka kuma yace gwamnatin kasarnan na cigaba da kokari wajen kawo karshen dukkanin tashe tashen hankula a kasarnan musamman ma rikicin manoma da makiyaya domin tabbatar da wanzuwar gabatar da addini.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here