An cafke mutum biyar da haramtaccen maganin a kurkura a Kano

0
523

Daga Sulaiman Auwal Mashal

A kokarin ta na kawar da yaduwar gurbatattun magunguna a Jihar Kano, hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu ta Jihar Kano Wato PHIMA karkashin jagorancin Dakta Usman Tijjani Aliyu tare da Hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya a matakin Farko karkashin Shugabacin Dakta Tijjani Husaini wanda kuma shine shugaban kwamitin karta kwana na Jihar Kano kan yaki da Annobar Covid19 dakuma hukumar kula da yancin masu sayen Kayayyaki itama bisa shugabancin Dakta Yusuf Muhammad Sabo sun kame kunshin wani magani mai suna Akurkura wanda yakai na daruruwan Nairori wanda aka shigo dasu Babisa ka’idaba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kayayyakin basu da Shedar rijista da hukumomin da Alhakin yin rijista ya shafa.

Kazalika An samu rahoton cewa wadanda sukayi Amfani da maganin sun tsinci kansu cikin yanayin rashin kwarin jiki da amai da Gudawa wanda har yakai ga an kaisu asibiti.

Haka kuma Akwai Mutane biyar dake da Hannu a shigo da magani tare da rarraba shi domin siyarwa Inda ake Saran gurfanar dasu kwanan nan da Zarar An Kammala gudanar da bincike a kansu.

Harma Shugabannin hukumomin da suka gudanar da sumamen kama wannan magani na Akurkura sukayi alkawarin cewa zasu cigaba wannan Aiki har sai sun kawar da masu wannan al’ada Daga Cikin Al’umma musamman ma Daga Cikin masu sayar da maganin gargajiya dana asibiti Domin tsaftace Jihar Kano Daga irin wadannan magunguna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here