Coronavirus : An sake gano masu cutar sama da 500 ranar Asabar a Najeriya

0
130

Daga Ahmed Muhammad

Mutum fiye da 500 ne aka tabbatar a ranar Asabar sun kamu da cutar korona a Najeriya.

Duka-duka adadin masu cutar yanzu 15,682 a ƙasar, a cewar hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta kasar, NCDC.

Jihohin Lagos da Kano da kuma birnin Abuja ne ke da rinjayen masu cutar cikin wannan ƙididdiga da hukumar ta fitar a daren Asabar ɗin nan.

Alƙaluman sun ce mutum 195 ne suka kamu da cutar a Lagos, jihar da annobar ta fi ƙamari a Najeriya.

A Abuja, babban birnin kasar, an samu sabbin waɗanda korona ta harba har mutum 50. Da wannan, adadin masu cutar a Abuja ya kai 1,212

Jihar Kano, wadda a ‘yan makwannin nan, yawan masu cutar ya yi matuƙar raguwa, an sake gano masu korona 42 ranar Asabar.

Adadin masu coronavirus a kasashen Afrika
Coronavirus: Abubuwan da ya kamata ku dinga yi
Coronavirus a Najeriya: Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

Hukumar NCDC ta ce a jihar Kaduna, an tabbatar da gano mutum 27 da suka sake kamuwa, sai Edo mai mutum 26. A Oyo sabbin masu korona 22 aka gano ranar Asabar

Jihar Imo, an ba da rahoton cutar ta sake harbin mutum 21, a Gpmbe, an sake gano mutum 17. Sai Binuwai da Enugu na da mutum 12 kowaccensu.

Delta da Anambra, alƙaluman NCDC sun nuna mutum 11 ne suka sake kamuwa a cikin kowaccensu. Ebonyi na da mutum goma.

Nasarawa da Ogun, mutum tara-tara, sai Bauchi mai mutum takwas. Kebbi, an gano mutum huɗu. Sai mutum uku-uku a jihohin Akwa-ibom da Jigawa da Katsina.

A Yobe da makwabciyarta Borno, an ba da rahoton samu mutum bi-biyu cikin kowaccensu. Kwara da Ondo, mutum ɗai-ɗai sun sake kamuwa da korona.

Haka zalika, NCDC ta ce annobar ta yi sanadin mutuwar mutum takwas ranar Asabar ɗin. Yayin da mutum 210 suka warke har kuma an sallame su daga cibiyoyin killacewa na ƙasar.

Muhimman bayanai kan annobar korona
An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

A ranar Juma’a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.

Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa’i da Seyi Makinde da kuma Okezie Ikpeazu duk sun kamu da annobar amma sun warke ban da gwamnan Abia wanda ya kamu da cutar a baya-bayan nan.

Jiha guda ce kawai ta rage yanzu a Najeriya cutar ba ta bulla cikinta ba wato jihar Cross Rivers.

Wasu dai na zargin cewa mai yiwuwa annobar ta shiga jihar, rashin yin gwaji ne ya sa aka ba a iya gano ta ba.

Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya yawan gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji fiye da dubu ɗaya cikin sa’a 24.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here