‘Trump na yunkurin tafka magudin zabe’

0
119

Daga Hannatu Sulaiman Abba

Dan takarar shugaban kasar Amurka a jam’iyyar Democrat Joe Biden ya zargi shugaban kasar Amurka Donald Trump da yunkurin “satar kuri’u” a zaben da za’a gudanar a ranar 3 ga watan Nuwamba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Democrat Biden ya tattauna a wata gidan talabijin akan zabemn da za’a gudanar bayan watanni biyar masu zuwa.

Ya bayyana cewa “babban abin fargaba a wannan zaben shi ne wannan shugaban kasar ka iya shirin satar kuri’u”

A cewarsa ”Wannan mutumin ya shirya zaben fitar da dan takara ta wasika a yayinda da yake zaune a ofishinsa, wannan irin zaben zamba ne bayayyanan ne.

Biden ya bayyana cewa idan Donald Trump ya fadi zaben amma ya ki yarda da shan kaye, yana da yakinin cewa manyan sojoji za su fitar da shi daga Fadar White House.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here