Gwamnan Kano Ganduje ya kaddamar da gwajin corona a gida gida

0
186

Daga Sulaiman Ramat

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya Kaddamar da gwajin cutar coronavirus a gida gida.

Aikin dai yana daga cikin aniyar gwamnatin Kano na gwada mutane dake unguwanni don kaucewa yaduwar cutar a fadin Jihar wanda aka gabatar a unguwar Wambai dake Dorayi Babba.

A Jawabinsa GwamnanKano Ganduje, ya tabbatar da Nasarar yaki da cutar a Jihar Kano wanda hakan ze kawo karshen cutar bada dadewa ba insha Allah.
Gwamna yasamu rakiyar Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Kwamishinonin Lafiya, Muhalli, Yada Labarai da masu bawa Gwamna Shawara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here