Home Manyan Labarai WATA SABUWA: Mahara sun kashe mutum 26 a harin Faskari, jihar Katsina

WATA SABUWA: Mahara sun kashe mutum 26 a harin Faskari, jihar Katsina

0
240

Kwana daya kacal bayan zanga-zangar da mazauna wasu kananan hukumomin jihar Katsina suka yi a dalilin rashin tsaro da ya addabi wannan jiha, a karamar hukumar Faskari ranar Talata, mahara sun afka wa mutane inda suka kashe mutum 26 sannan wasu mutum 20 suka jikkata.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar, Gambo Isah ya sanar da haka da yake tabbatar da aukuwar wannan mummunar hari ga manema labarai a Katsina.

Isah ya ce akalla mahara 200 akan babura ne suka dirawwa kauyen Kadisan dake karamar hukumar Faskari a ranar Talata, kuma sun kashe mutum 20 nan take.

” Maharan sun yi kokarin yi wa mutanen kauyen kwacen abinci da sace sace sai suka ki yarda hakan ya faru. Daga nan ne suka bude musu wuta babu kakkautawa har suka hallaka mutum 20 nan take.

” Mutum 26 su samu rauni da a ranar Laraba shida suka ce ga garin ku nan.

Isah ya ce zaratan ‘yan sandan da suka zo daga Abuja sun samar da zaman lafiya a kananan hukumomin Batsari, Safana da Jibiya.

” Yanzu babu sauran fargaba a wadannan yankuna. Mutane za su rika barci idon su rufe babu matsala. Sannan kuma suma maharan da suka addabi yankin Faskari Sabuwa da Dandume za su kuka da kan su nan ba da dadewa ba domin zaratan dakarun Najeriya na gab da diran musu babu kakkautawa.

Isah ya kara da cewa yanzu haka jami’an tsaro na aikin samar da tsaro a wadannan yankuna dake jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here